Gobara ta Kona Dakin Ajiyan Kayayyakin Abinci na Kamfanin Sumal Foods Limited

 

Yanzu muke samun mummunan labarin yadda gobara ta kama dakin ajiyan kayayyakin abinci a kamfanin Sumal Foods Limited.

A cewar rahoton Punch, gobarar ta tashi ne a ma’ajiyar kayan abincin kamfanin da ke unguwar masana’antu na Oluyele da ke birnin Ibadan a jihar Oyo.

An ce gobarar ta fara ne da sanyin safiyar yau Laraba 25 Janairu, 2023, kamar yadda rahoto ya bayyana.

Ya zuwa yanzu dai babu cikakken bayanai na abin da gobarar ta ci da kuma halin da ake ciki na tashin hankali.

Karin bayani na nan tafe…

bella naija news

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here