Shugaba Buhari Kaka ne Wanda ya Dace ya Gane Cewa Kasar Nan Rushewa ta ke yi – Gwamna Ortom

Gwamnan jahar Binuwai, Samuel Ortom, ya yi kira ga shugaba Buhari da ya gaggauta daukar mataki domin Najeriya tana ragargajewa ne a halin yanzu.

Ortom ya bayyana cewa, yana matukar kaunar Buhari amma a yanzu lokaci ne da ya dace a fada masa gaskiya kuma ya dauka mataki.

Gwamnan arewan ya ce tabbas Buhari uba ne ga wasu, ga wasu kuwa kaka ne yayin da wasu suke tattaba kunnensa, don haka ya dace ya gane halin da ake ciki.

Benue – Samuel Ortom, gwamnan jahar Binuwai, ya ce shugaban kasa kaka ne wanda ya dace ya gane cewa kasar nan rushewa ta ke yi sakamakon al’amuran ‘yan ta’adda, TheCable ta rawaito.

A sakon da ya aike wa shugaban kasa Buhari a ranar Asabar domin taya shi murnar cika shekaru 79 a duniya, Nathaniel Ikyur, sakataren yada labarai na Ortom, ya sanar da cewa gwamnan ya ce rashin tsaron da ya addabi mutane ba shi ba ne alkawarin shugaban kasar yayin da ya hau mulki.

TheCable ta rawaito cewa, kamar yadda takardar tace, gwamnan wanda ya ce ya na kaunar Buhari, ya yi kira ga shugaban kasa da ya dauka matakin gaggawa domin tsare kasar nan kafin ya bar kujerarsa.

“Na bi sahun iyalanka, abokai, abokanan siyasa da dukkan ‘yan Najeriya domin taya ka murnar cika shekaru 79 a duniya,” yace

“Ga wasu, shugaban kasa uba ne, ga wasu kuwa kaka ne yayin da wasu kuwa tattaba kunne sukeg are shi wanda ya dace ya gane cewa Najeriya rushewa ta ke yi sakamakon ta’addancin ‘yan bindiga wadanda ke cigaba da tarwatsa tubalin hadin kan kasar nan.

“A kowacce rana, ana yanka jama’a kamar dabbobi a gonakinsu, a gida ko kuma a babbaka su yayin da suke kan hanyarsu ta zuwa wani wuri.Ga fuskokin ‘yan ta’addan tasa a bidiyo amma babu wanda aka kama.

“Tituna sun zama tarkuna inda ‘yan kasa ke tsoron bi saboda tsoron kada a sace su ko kuma a kashe su. Wannan budadden sirri ne tunda babu wanda ya tsira a kasar nan.”

Gwamnan ya ca tsarin tsaron kasar nan ya lalace kuma ‘yan kasa suna rayuwa a cikin tsoro.

“Kada shugaban kasa ya saurari mahaukata wadanda ba su fada masa gaskiya, suna ce masa komai daidai. “Babu abinda ya ke daidai a Najeriya a halin yanzu shugaban kasa.

Dole ne ka dauka matakin gaggawa yanzu domin janye kasar nan daga halin da ta ke ciki kafin lokaci ya kure,” yace.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here