Shugaba Buhari ya Sake Nada Farfesa Oloyede a Matsayin Shugaban Hukumar JAMB
Ma’aikatar Ilimi ta sanar da manyan nade-nade guda uku da Shugaba Buhari ya amince da su.
An sake nada Farfesa Oloyede a matsayin Shugaban hukumar JAMB yayin da aka sake nada Farfesa Rasheed a matsayin Shugaban NUC a karo na biyu.
Buhari ya kuma amince da sake nada Isiugo-Abanihe a matsayin Shugaban NABTEB yayin da aka nada Farfesa Mebine a matsayin sabon DG na Cibiyar Lissafi ta Kasa.
FCT Abuja – Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sake nada Ishaq Oloyede a matsayin Shugaban Hukumar Samar da Guraben Karatu a Manyan Makarantu ta Kasa (JAMB) a wa’adi na biyu na shekaru biyar.
Read Also:
Jaridar The Nation ta rawaito cewa shugaban kasar ya kuma amince da nadin Farfesa Abubakar Rasheed a matsayin Shugaban Hukumar Kula da Jami’o’i ta Kasa (NUC) da Hamid Bobboyi a a matsayin Babban Sakataren Hukumar Kula da Ilimin Bai-daya ta Kasa (UBEC).
Legit.ng ta tattaro cewa kakakin ma’aikatar ilimi ta tarayya, Ben Bem Goong ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa a ranar Juma’a, 20 ga watan Agusta.
Shugaba Buhari ya kuma amince da sake nada Farfesa Ifeoma Isiugo-Abanihe a matsayin shugaban Hukumar Shirya Jarrabawar Kasuwanci da Fasaha ta Kasa (NABTEB) na wa’adi na biyu na shekaru hudu, Aminiya ta rahoto.
Sanarwar ta ce nadin na Oloyede da Rasheed ya fara aiki ne daga ranar Lahadi, 1 ga watan Agusta, nadin Bobboyi zai fara aiki daga ranar Asabar, 21 ga watan Agusta.