‘Yan Bindiga Sun yi Garkuwa da Malamai 2 na Jami’ar ABSU a Jahar Abia

 

‘Yan bindiga sun sace wasu mutane ciki har da malaman jami’ar ABSU ta jahar Abia.

‘Yan bindigan sun sace su ne yayin da suka tare hanya suna yi wa mutane fashi da makami.

Shugaban kungiyar ASUU, reshen ABSU, V.U. Nkemdirim ya tabbatar da lamarin ya kuma ce an sanar da hukumomin tsaro.

Wasu da ake zargin yan bindiga ne sun sace malamai biyu na Jami’ar Jahar Abia, ABSU, da ke Uturu da wasu mutanen a kan hanyar ABSU-Isuikwuato, News Wire NGR ta rawaito.

Shugaban kungiyar malaman jami’o’i, ASUU, reshen jami’ar ABSU, V.U. Nkemdirim ne ya sanar da sace su a ranar Juma’a.

A cewar Nkemdirim, lamarin ya faru ne misalin karfe 6 na yamma a ranar Alhamis kamar yadda News Wire NGR ta rawaito.

Ya ce wadanda aka sace din sune Rebaran Farfesa S.O. Eze na tsangayar Industrial Chemistry da kuma wani malamin coci, kuma malami a tsangayar koyar da fasahar sadarwa, Chris Afulike.

Ta yaya aka sace malaman?

An ce kowannensu na tafiya a motarsa daban ne yayin da suka fada hannun yan bindigan da suke tare hanya suna yi wa matafiya fashi. Malamin jami’ar ya ce: “Bayan fashin, yan bindigan sun yi awon gaba da malaman jami’an biyu da wasu mutane.

“Kawo yanzu ba a san inda suke ba. Amma, an gano motar Dr Chris Afulike kirar Toyota Camry da wayarsa ta salula a cikin motar.”

Nkemdirim ya kara da cewa iyalan malaman jami’an sun tabbatar da afkuwar lamarin, kuma mahukunta a jami’ar suma suna bada gudunmawa domin ganin yadda za a ceto su.

latest nigerian news papers

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com