‘Yan Bindiga Sun Kashe Manoma 5 a Jahar Osun

 

‘Ƴan bindiga sun kashe manoma biyar a hanyarsu na zuwa gonakinsu a kauyen Toro a jahar Osun.

Wani mazaunin garin ya tabbatar da lamarin yana mai cewa wadanda aka kashe yan asalin garin Modakeke ne

Rundunar yan sandan jahar Osun ta bakin kakakinta, ta ce ta samu labarin kashe mutanen kuma an tura jami’ai yankin.

Wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kashe mutane biyar yan asalin garin Modakeke a jahar Osun kamar yadda The Punch ta rawaito.

The Punch ta ruwaito cewa mutanen biyar suna kan hanyarsu na zuwa gonakinsu na a kauyen Toro a ranar Juma’a 20 ga watan Agusta yayin da yan bindigan suka kashe su.

Wani jagoran al’umma a Modakeke ya tabbatar da kisan

Wani jagoran al’umma a garin Modakeke mai suna Mr Femi Eluyinka, wanda ya tabbatar wa The Punch afkuwar lamarin ya ce wasu mutanen garin da ‘yan sanda sun kwashe gawarwarkin mutanen.

Mr Eluyinka ya ce kisan ya janyo zaman dar-dar a garin tare da tada hankulan mutane.

Ya ce:

“Jami’an yan sanda sun iso. Hankulan mutane ya tashi. Dukkansu biyar yan asalin garin Modakeke ne kuma an kashe su ne a safiyar yau a kan hanyar Toro. Suna hanyarsu ne zuwa gonakinsu.”

Da aka tuntube shi domin ji ta bakinsa, Mai magana da yawun rundunar yan sandan jahar Osun, Mr Yemisi Opalola ya ce:

“Mun samu labarin cewa an kashe wasu mutane kuma kwamishinan yan sanda ya tura karin jami’ai zuwa yankin.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here