Hoton Femi Fani Kayode, Gwamnoni da Ministoci a Gurin Daurin Auran ‘Dan Shugaba Buhari

 

Femi Fani-Kayode ya bi sahun manyan ‘yan APC don halartan daurin auren dan Shugaban kasa, Yusuf Buhari a jahar Kano.

Fani Kayode ya kasance babban mai sukar gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Za a kulla aure tsakanin Yusuf da Zahra Bayero a yau Juma’a, 20 ga watan Agusta.

Bichi, jahar Kano – Femi Fani-Kayode, tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, ya shiga cikin wasu manyan jiga-jigan ‘yan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) domin daurin auren dan Shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Mun kawo a baya cewa dan Shugaba Buhari daya tilo, Yusuf zai auri diyar Alhaji Nasir Ado Bayero, Sarkin Bichi a yau Juma’a, 20 ga watan Agusta.

Garin ya riga ya cika ya tumbatsa sannan kuma jami’an tsaro sun mamaye manyan wurare a duk faɗin Kano.

A wasu hotuna da ya wallafa a kafafen sada zumunta, an ga Fani-Kayode, babban mai sukar gwamnatin Buhari, tare da wasu manyan ‘yan APC.

Wasu daga cikin gwamnonin da aka gani da FFK sune Babagana Zulum (Borno) da Bello Matawalle (Zamfara). Isa Pantami, Ministan sadarwa da tattalin arziki na zamani, shi ma ya ɗauki Hoto tare da Fani-Kayode.

Ya wallafa a shafinsa na Instagram:

“Na dira Kano tare da abokaina da ‘yan uwana Gwamna Bello Matawalle na jahar Zamfara, Gwamna Babagana Umar Zulum na jahar Borno, Sanata Sani Ahmed Yarima, Sanata Ali Ndume, Ambasada Bashir Yuguda, Hon. Minista Isa Pantami, Mallam Nuhu Ribadu da sauran su domin daurin auren dan shugaban kasa Muhammadu Buhari, Yusuf Buhari, da diyar Sarkin Bichi, HRH Nasiru Ado Bayero, Zahra Ado Bayero. ”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here