Daurin Auran Yusuf Buhari: Mataimakin Shugaban Kasa, Osinbajo ya Dira Jahar Kano

Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya dira a jahar Kano domin daurin auren dan shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Osinbajo ya samu tarba ne daga gwamnan jahar, Abdullahi Umar Ganduje, suna kuma jiran saukar Shugaba Buhari wanda zai taso daga Yola.

Za a dai kulla aure tsakanin Yusuf Buhari da ‘yar sarkin Buchi a yau Juma’a, 20 ga watan Agusta.

Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya isa filin jirgin sama na Aminu Kano da ke jahar Kano domin daurin auren dan shugaban kasa Muhammadu Buhari. Yusuf, da daya tilo da Shugaba Buhari ya mallaka, zai auri Zahra, diyar Alhaji Nasir Bayero, Sarkin Bichi.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Kano ne ya tarbi mataimakin shugaban kasar.

Shugabannin biyu tare da wasu manyan jami’an gwamnati suna jiran shugaban kasa, wanda ake sa ran zai tashi daga Yola, babban birnin jahar Adamawa, kowane lokaci daga yanzu.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here