Shugaba Buhari ya yi Sababbin Nade-Nade a Hukumomin ICPC da RMAFC

 

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi sababbin nade-nade masu muhimmanci a hukumomin ICPC da RMAFC.

A hukumar yaki da cin hanci da rashawa, shugaban kasar ya bukaci majalisar dattijai ta tabbatar da kwamishinoni biyar da za su cike guraben ayyuka.

Hakazalika Buhari ya nemi a tabbatar da wani wanda aka zaba a matsayin Kwamishinan Tarayya na Hukumar tattara kudaden shiga (RMAFC).

Abuja – Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci majalisar dattijai ta tabbatar da kwamishinoni biyar da za su cike guraben ayyuka a hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta ICPC.

Ya kuma bukaci Majalisar Tarayyar da ta tabbatar da wani wanda aka zaba a matsayin Kwamishinan Tarayya na Hukumar tattara kudaden shiga (RMAFC).

Jaridar The Nation ta rawaito cewa buƙatun shugaban kasar na ƙunshe ne a cikin wasiƙu biyu mabanbanta da shugaban majalisar dattawa, Ahmad Lawan ya karanta a zauren majalisar.

Shugaba Buhari a daya daga cikin wasikun ya bayyana cewa bukatarsa ta tabbatar da wadanda ya zaba a hukumar ICPC ya yi daidai da tanadin sashe na 3 (6) na Dokar Cin Hanci da Rashawa da Sauran Laifuka makamanta, 2000.

Wadanda aka zaba don mukamin a ICPC sun hada da:

1. Dr. Mojisola Yaya-Kolade, Ekiti (Kudu maso Yamma)

2. Misis Anne Otelafu Odey, Cross River (Kudu maso Kudu)

3. Alhaji Goni Ali Gujba, Yobe (Arewa maso Gabas)

4. Dr. Louis Solomon Mandama, Adamawa (Arewa maso Gabas)

5. Sanata Anthony O. Agbo, Ebonyi (Kudu maso Gabas).

A wani lamari makamancin haka, Buhari a wata wasika ta biyu ya nemi Babban Majalisar ta tabbatar da nadin Engr. Mohammed Sanni Baba a matsayin Kwamishinan Tarayya na Hukumar tattara kudaden shiga, mai wakiltar Jahar Bauchi.

A cewar Shugaban kasar, an gabatar da bukatar tabbatar da wanda aka zaba ne bisa tanadin sashe na 154 (1) na kundin tsarin mulkin 1999 na Tarayyar Najeriya (kamar yadda aka yi wa gyara).

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here