An yi Garkuwa da Kansilan ƙaramar Hukumar Eket Dake Jahar Akwa Ibom

 

Rundunar yan sanda reshen jahar Akwa Ibom, ta tabbatar da sace kansilan gunduma ta 6 dake ƙaramar hukumar Eket.

Rahotanni sun bayyana cewa wannan shine karo na uku a cikin makonni uku ana aikata masa haka.

Kwamishinan yan sandan jahar, Andrew Amiengheme, ya bada umarnin gudanar da bincike kan lamarin sace kansilan.

Akwa Ibom – Rundunar yan sanda ta tabbatar da sace kansilan guduma ta 6 a ƙaramar hukumar Eket, jahar Akwa Ibom, ranar Talata, kamar yadda Vanguard ta rawaito.

Kakakin yan sandan jahar, SP Odiko Macdon, shine ya tabbatar da faruwar harin ga hukumar dillancin labarai ta ƙasa (NAN) a Eket.

Yace maharan sun sace kansilan ne a harabar gidan mai ranar Asabar, 25 ga watan Satumba, da misalin karfe 8:00 na dare.

Kwamishina ya bada umarnin bincike

Macdon ya bayyana sace kansilan da babban abun takaici kuma hukumar yan sanda ba zata lamurta ba, yace:

“Kwamishinan yan sanda, Andrew Amiengheme, ya bada umarnin gudanar da bincike kan lamarin.”

“Tabbas mun samu rahoto, kuma mun fara aiki kan lamarin, bincike ya yi nisa kuma ba zan ɓoye gaskiya kan cewa muna da masaniya a lamarin ba.”

“Binciken mu ya yi nisa sosai kuma ba tare da jimawa ba zamu ceto shi. Bana son fallasa abubuwan da binciken mu ya gano domin tabbatar da mun cimma nasara.”

Yan sanda zasu tabbatar da kamo maharan

Kakakin yan sandan ya tabbatar da cewa hukumarsu zata yi duk mai yuwuwa wajen tabbatar da an hukunta waɗanda suka aikata garkuwa da kansilan, kamar yadda Punch ta rawaito.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here