Zanga-Zanga: Jami’ar BUK ta Dakatar da ɗaukar Darussa

Hukumar gudanarwar Jami’ar Bayero da ke jihar Kano ta sanar dakatar da ɗaukar darussa zuwa wani lokaci sakamakon zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa da ake ci gaba da yi a faɗin Najeriya.

Wata sanarwa da Jami’ar ta fitar yau Litinin, ta ce ta ɗauki matakin ne bayan zama da ta yi da duba batun zanga-zangar da ake yi.

“Mun damu da lafiyar ɗalibai da kuma dukiyoyinsu shi ya sa muka ɗauki matakin, don haka muke yin kira ga ɗalibai da ma’akatanmu da su ci gaba da kula da irin zirga-zirgar da za su yi a wajen jami’a domin kaucewa shiga haɗari,” in ji sanarwar Jami’ar.

BUK ta kuma shawarci ɗaliba da ke zama cikin makarantar da su kwantar da hankali da kuma bin doka da oda.

Ta ce za a koma ɗaukar darusa da zarar al’amura sun daidaita.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here