ƙasar Chadi na Shirin Tura Sojoji Dubu 1 Zuwa Mali
Ma’aikatar harkokin wajen Mali ta bayyana cewa ƙasar Chadi na shirin tura mata ƙarin sojoji dubu domin taimaka mata yaƙi da masu iƙirarin jihadi a daidai lokacin da Faransa ke rage yawan sojinta a ƙasar.
Sojojin da ke mulkin Mali sun yi murna da wannan matakin na Chadi.
Read Also:
Ana dai kallon sojojin Chadi a matayin waɗanda ke ƙoƙari a yaƙi da masu iƙirarin jihadi.
Wannan yunƙurin na gwamnatin Chadi na zuwa ne a daidai lokacin da Faransa ke ƙoƙarin shawo kan sauran ƙasashen duniya domin kai sojoji yankin Sahel.
Tuni Faransa ta rufe sansanoni uku na sojinta da ke Mali a bana haka kuma nan da watanni masu zuwa za ta janye wasu dakarunta dubu 5000.
Sakamakon irin ƙarin hare-haren da ake samu a Mali da Burkina Faso da Nijar, mutane na ƙara saka ayar tambaya kan tasirin ƙasashen waje a yaƙi da masu iƙirarin jihadi.