Gwamnatin Jahar Borno ta Sake Samun Dalibar Chibok 1 da Yaranta 2

 

Bayan shekara 7, an sake gano daya daga cikin yan matan makarantar Chibok.

An aurar da ita ga daya daga cikin yan ta’addan Boko Haram kuma har ta haifi yara biyu.

Sama da yan Boko Haram 100 sun mika wuya kwanan nan.

Gwoza, Borno – Gwamnan jahar Borno, Babagana Umara Zulum, ya karbi bakuncin daya daga cikin yan matan makarantar Chibok da aka sace tun shekarar 2014 sun zana jarabawar karshe.

Sojojin Najeriya da suka kai matar wajen gwamnan ranar Asabar a garin Gwoza sun ce ita ta mika kanta ga hukuma.

Zulum ya bayyana hakan a jawabin da ya saki a shafinsa na Facebook.

Dalibar mai suna Hassana Adamu, tare da yaranta biyu sun hadu da Gwamna Zulum lokacin da kwamandan 26 taskforce Brigade, Janar DR Dantami, ya kai ta.

Hassana na cikin dalibai mata kimanin 276 da akayi awon gaba da sy daga daga makarantar sakandaren mata dake Chibok, jahar Borno.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here