Tsofaffin Takardun Kuɗi: Kotun ƙoli ta ce a Ci gaba da Amfani da N200, N500 da N1000
Kotun ƙolin Najeriya ta yanke hukuncin cewa za a ci gaba da amfani da tsofaffin kuɗin ƙasar har zuwa 31 ga watan Disamban 2023.
A lokacin da ta yanke hukuncin, kotun ta ce ba a sanar da al’umma da wuri ba, kamar yadda dokar Babban Bankin Najeriya ta tanada kafin shugaban ƙasa ya bayar da umarnin sake fasalin kuɗin da kuma janye tsofaffi daga hannun al’umma.
Saboda haka kotun ta ce umurnin ba ya kan doka, sannan aiwatar da shi haramun ne.
Tawagar masu yanke hukuncin bakwai ne suka yi zaman kotun ƙolin kuma suka amince a ci gaba da amfani da N1000 da N500 da kuma N200 a matsayin kuɗin ƙasa har sai nan da ranar 31 ga watan Disambar wannan shekarar.
Kotun ta kuma soke matakin Gwamnatin Tarayya na sake fasalin naira, tana cewa matakin ya ci karo da kundin tsarin mulki na 1999.
Tun da fari gwamnonin jihohin Kaduna da Kogi da kuma Zamfara ne suka shigar da gwamnati ƙara, kuma ƙarar da suka shigar aka yi amfani da ita a matsayin hujja wajen yanke wannan hukunci.
A watan jiya kuma wasu gwamnoni suka ƙara bin bayansu wajen shigar da ƙarar, abin da ya janyo kotun ƙolin ta dakatar da wa’adin na wucin gadi da aka sanya na daina amfani da tsofaffin kuɗin.
A hukuncin da ya yanke a ranar Juma’a mai shari’a Emmanuel Agim, ya ce sahalewar da Shugaba Buhari ya yi wa CBN na janyo takardun tsofaffin kuɗi ba daidai ba ne.
“Duba da bayanan da aka gabatar, Na fuskani ba a bai wa al’umma wani wa’adi ba na azo a gani ba, kamar yadda sashe na 20 na dokar CBN ta 2007 ya bayyana, gabanin shugaban ƙasa ya bayar da umarnin sake fasalin naira da janye tsofaffin takardun. A don haka, yanzu umarnin da shugaba ya bayar ba daidai ba ne kuma aiwatar da sauyin shi ma ba ya kan daidai.” Kamar yadda ya yi bayani.
A baya bayan nan ne Shugaba Buhari ya bai wa CBN umarnin sake fito da tsohuwar takardar kuɗi ta N200 domin ci gaba da amfani da ita har zuwa ranar 10 ga watan Afirilu, domin sassauta halin da ‘yan ƙasar suka tsinci kansu na rashin samun sabbin takardun naira.