Nasarar Tinubu Nufin Allah ne – Aisha Buhari

Mai ɗakin shugaban Najeriya, Aisha Buhari, ta kwatanta nasarar Bola Tinubu na jam’iyyar APC a zaɓen shugaban ƙasa da aka kammala da cewa nufi ne na Allah.

Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya ya ruwaito cewa Aisha Buhari ta bayyana haka ne lokacin da ta karɓi bakuncin uwar gidan zaɓaɓɓen shugaban ƙasa Sanata Oluremi Tinubu da mai ɗakin zaɓaɓɓen mataimakin shugaban ƙasa, Hajiya Nana Shettima, a wani ziyarar godiya da suka kai mata.

Ta ce “duk da bambance-bambance na ra’ayi, mu karɓi nasarar da cewa nufi ne na Allah”.

Tun da farko Sanata Oluremi Tinubu ta faɗa wa mutane da suka taru cewa sun je faɗar shugaban ƙasa ne domin gode wa mai ɗakin shugaba Buhari saboda irin goyon baya da ta basu wajen ganin APC ta samu nasara a zaɓen shugaban ƙasa da aka gudanar.

Zaman ya samu halartar matan wasu gwamnonin APC da ƙawayen matar shugaban ƙasar.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here