Ba za mu ƙalubalanci Sakamakon Zaɓen Tinubu ba – SDP

Jam’iyyar SDP mai adawa a Najeriya ta ce ba za ta kalubalanci sakamakon zaɓen shugaban ƙasa da hukumar zaɓe ta sanar ba wanda ya bai wa Bola Tinubu nasara.

Shugaban jam’iyyar Shehu Gabam, shi ya bayyana haka a wani taron manema labarai a Abuja jiya Alhamis.

“Duk da cewa an samu kura-kurai a zaɓen, SDP ba za ta kalubalanci nasarar Tinubu ba na jam’iyyar APC a matsayin zaɓaɓɓen shugaban ƙasa,” in ji Gabam.

Ya ce jam’iyyar ta yi na’am da zaɓin ‘yan ƙasa kuma sun amince da sakamakon zaɓen.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here