Za a Ci gaba da Harkokin Zirga-Zirgan Jirgin ƙasan Abuja-Kaduna Cikin Watan nan – Ministan Sufuri
Abuja – Ministan sufuri, Mu’azu Sambo, ga bayyana cewa a wannan watan na Nuwamba da mukee ciki ake shirin ci gaba da harkokin zirga-zirgan Jirgin ƙasa a layin dogon Kaduna zuwa Abuja.
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa ba ya ga haka, gwamnati ta shirya sintirin tsaro a layin dogon na tsawon awanni 24 kowace rana da nufin kare sake kai hari.
Ministan ya sanar da haka ne a babban birnin tarayya Abuja yayin da yake zayyana ayyukan ma’aikatar sufuri tun daga shekarar 2015 zuwa yau.
Read Also:
Yace sun shirya ingantaccen kuma isasshen tsaro domin tabbatar da tsare rayukan fasinjoji amma bai faɗi ainihin ranar da zirga-zirgan jirgin ƙasan zata ci gaba ba.
Sambo ya ƙara da cewa ma’aikatar Sufuri ta ɗauki darasi a harin da ‘yan ta’adda suka kai a watan Maris, wanda ya haddasa dakatar da Sufurin jirgin ƙasa a Titin Kaduna-Abuja.
Ministan ya sanar da cewa a yanzun an sanya wasu na’uroro a Layin dogon domun sa ido kan duk wata halitta da zata gitta a kan titin, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.
A cewarsa, na’urar zata bai wa shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ma’aikatu da sauran ɓangarorin da lamarin da shafa da ma hukumomin tsaro damar ganin abinda ke wakana a kan titin ba tare da jinkiri ba.
Ku dakaci karin bayani…