Tsohon ‘Dan Majalisar Jihar Kaduna Mai Wakiltar Mazabar Kudan, Alhaji Danlami ya Rasu

 

Alhaji Danlami Dan Inna Likoro, tsohon ‘dan majalisar jihar Kaduna da ya wakilci mazabar Kudan ya kwanta dama.

Dan Inna ya rasu a yammacin Lahadi bayan yayi fama da gajeriyar rashin lafiya bayan gwagwarmaya da yayi yana raba Zakka.

‘Dan Takarar Gwamnan Kaduna a PDP, Ashiru Isah Kudan ya kwatanta rasuwarsa da babban rashi a lokacin da jam’iyyar ke matukar bukatarsa da gogewarsa.

Kaduna – Tsohon ‘dan majalisa da ya wakilci mazabar Kudan a majalisar jihar Kaduna tsakanin 2011 zuwa 2019, Alhaji Danlami Dan Inna Likoro, ya kwanta dama.

A yayin tabbatar da faruwar lamarin, iyalan tsohon ‘dan majalisar sun ce ya rasu da yammacin Lahadi sakamakon gajeriyar rashin lafiya kuma ya dinga aikin bayar da Zakkah kafin lokacin, jaridar Daily Trust ta rahoto .

Har zuwa rasuwarsa, Likoro shi ne ‘dan takarar kujerar da ya bari na yankinsa a karkashin jam’iyyar PDP.

‘Dan Takarar Gwamna Yayi Ta’aziyya

A sakon ta’aziyya ta bakin hadiminsa na fannin yada labarai, Shuaibu Gimi, ‘dan takarar kujerar gwamnan jihar Kaduna a jam’iyyar PDP, Alhaji Isah Ashiru Kudan, ya kwatanta tsohon ‘dan majalisar da gogaggen ‘dan siyasa da ya bayar da gudumawa wurin ganin cigaban jam’iyyar da jihar Kaduna.

Ashiru ya bayyana cewa, marigayin ya mayar da hankali wurin ganin cigaban jam’iyyar kuma yana da rikakkun ra’ayin damokaradiyya wanda ya rasu yayin da jam’iyya ke matukar bukatar gudumawarsa da gogewarsa.

Daily Trust ta rahoto cewa, ya jajantawa iyalansa da dukkan iyalan PDP na kasar Najeriya ballantana reshen jihar Kaduna.

 

naija papers

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here