Rashin Ayyukan yi: Muna Cikin Matsala a Kasar Nan – Chris Ngige

 

Ministan Kwadago na Najeriya Chris Ngige ya ce karuwar rashin ayyukan yi na zame wa kasar barazana.

Jaridar Punch ta ce ministan ya fadi hakan ne a ranar Talata yana mai alakanta matsalar da rashin ilimin da ya yi wa Najeriyar katutu, yana mai gargadin cewa idan ba a magance matsalar ba, to kasar na iya “rushewa gaba daya.”

Ministan ya bayyana hakan ne a wajen taron hadin gwiwa kan tattalin arziki da Ma’aikatar Ayyuka Na Musamman ta shirya a Abuja, babban birnin Najeriyar.

Minista Ngige ya ce, “Muna cikin matsala a kasar nan. Muna cikin matsala kuma duk wanda ya gaya muku cewa bai san muna cikin matsala ba to karya yake yi wa kansa.

“Muna cikin wata matsala da take a zagaye, daya na bin daya. Ya rage ga ni da ku da wadanda ake damawa da su, mu yi shawarar yadda za mu ceci kanmu, da ‘ya’yanmi da kasarmu.

“Idan muka ci gaba da tafiya kan wadannan matakan da ake kai; sayan harsasai da dasa wa mutanen nan bam da dasa wa ‘yan Boko Haram bam da dasa wa masu satar mutane bam, to asarar kudi da lokaci za a yi.

“Amma idan ka dauki matakan kariya, ba za ka yi asarar kudi sosai ba. Dole mu bai wa mutanen nan ilimi tun daga can kasa.

“Wadanda ba su da hanyar samun ilimi kuma, dole mu ba su ayyukan yi don su dogara da kansu. Su rufa wa kawunansu asiri,” a cewar ministan.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here