Bincike ya Gano Dutse Mai Zanen Rakumi a Saudiyya

 

Wani sabon bincike ya gano wasu duwatsu na tarihi masu zanen rakuma da jakuna a arewacin Saudiyya, wanda hakan ya sa suka zama irinsu mafi tsufa da aka samu a duniya.

Binciken ya ce an fara gano su ne a karon farko tun shekara uku da suka gabata, kuma an yi kiyasin sun fi shekara 2,000 saboda kamanceceniyarsu da irin abin da aka gano a birnin Petra na kasar Jordan.

Amma wani binciken da aka kammala a baya-bayan nan kan duwatsu da kasusuwan dabbobi da aka samu a wajen, sun nuna cewa duwatsun za su kai kusan shekara 7,000 ko 8,000.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here