Ana Amfani da Jirage Masu Zaman Kansu Wajen Safarar Zinare ba Bisa ƙa’ida ba a Najeriya – Dakta Uche Ogah

 

Ministan hakar albarkatun ƙasa, Dakta Uche Ogah, ya bayyana irin ta’adin da ake yi ta hanyar amfani da jirage masu zaman kansu.

Ogah yace dole sai an samar da hukunci mai tsauri kan duk waɗanda aka damke da hannu a safarar zinari ba bisa ka’ida ba.

Hakazalika ya bayyana wasu matakai da matukar aka bi su za’a kawo karshen hakar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba da safararsu.

Abuja – Karamin ministan hakar ma’adanai, Dakta Uche Ogah, ya bayyana cewa ana amfani da jirage masu zaman kansu wajen safarar zinare ba bisa ƙa’ida ba a Najeriya, kamar yadda dailytrust ta rawaito.

Ministan ya faɗi haka ne a wani zama don ji kan dala biliyan $9bn da aka rasa ta hanyar fasa kwaurin zinari da kuma hako ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba.

Kwamitin albarkatun ƙasa da hakar ma’adanai na majalisar dattijan Najeriya, shine ya shirya taron a Abuja.

Ministan ya bukaci a hukunta duk wani mai hannu kan aikata irin wannan laifin, Dakta Ogah yace:

“Ana amfani da jirage masu zaman kansu wajen satar zinari, wannan dalilin yasa wajibi a sanya ido kan masu jiragen sama da ayyukan jiragen.”

Me satar zinare zai jawo wa Najeriya?

Ministan ya kara da cewa smogan zinari da hakar ma’adanai ba bisa doka ba yana ƙara janyo wa Najeriya asarar biliyoyin daloli duk shekara.

A cewar ministan, lamarin na ƙara yawa ne saboda haɗin kan hukumomin tsaro da masu aikata laifin, haɗin kan al’ummar yankunan dake da albarkatun, karancin fasahar zamani da kuma rashin kishin ƙasa da yan Najeriya ke nunawa.

Ta wace hanya za’a magance matsalar?

This day ta rahoto, Ministan yace:

“Idan anason kawo karshen wannan laifin, wajibi a ɗauki matakan hukunci mai tsauri kan duk wanda aka kama da hannu.”

Ya kuma kara da cewa za’a iya magance matsalar ta hanyar samar da yan sandan hakar ma’adanai, kotu na musamman ko kuma masu hukunta laifuka, ƙara kasafin ma’aikata da kuma kishin ƙasa daga wurin yan Najeriya.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here