Mai Mota ya Mari Direban Keke Napep Wanda ya yi Sanadiyyar Mutuwarsa a Ilorin

 

Wani mai motar alfarma da bata jin harsashi ya shararawa direban keke Napep mari, wanda ya yi sanadiyyar mutuwarsa a Ilorin.

Rahotanni sun nuna cewa ɗan napep ɗin ya yi wa mai motar laifi na fasa masa fitila ta kimanin N2,500, amma ya nemi alfarmar zai biya N2,000.

Kakakin rundunar yan sanda reshen jahar Kwara, Ajayi Okasanmi, ya tabbatar da faruwar lamarin a yankin Garin Alimi, Ilorin.

Kwara – Wani direban motar alfarma wadda harsashi baya ratsa ta, Kayode Oluwatomi, ya laƙaɗawa ɗan nafef, Kola Adeyemi, duka har ya mutu a Ilorin jahar Kwara, kamar yadda Punch ta rawaito.

Rahotanni sun bayyana cewa direban Nafef ɗin ya buga wa mutumin, lamarin da ya jawo lalacewar fitilar yin fakin.

Legit.ng Hausa ta gano cewa lamarin ya auku ne ranar Litinin da misalin ƙarfe 5:00 na yamma a yankin Gerin Alimi, cikin garin Ilorin.

Mai Napep, Adeyemi, ya bugi motar ta alfarma mai lamba BX 954 AJL a baya, lamarin da ya jawo fasa fitilar aje mota, wanda ake siyarwa N2,500.

Shin ɗan napep din ya biya kuɗin?

Wani shaidan gani da ido, wanda ya ɓoye sunansa, yace direban nafef ya roki alfarma zai biya N2,000 na ɓarnar da yayi, amma mai motar yaƙi amincewa.

Mutumin yace:

“Nan take rikici ya ɓarke tsakaninsu, mai motar ya ɗaga hannu ya mari ɗan napep ɗin da wani abu da ake zargin zobe ne ko laya, nan take ya faɗi kasa warwas.”

“Daga baya an tabbatar da ɗan nafef ɗin ya rigamu gidan gaskiya a asibitin Garin Alimi dake Ilorin.”

Wane mataki yan sanda suka ɗauka?

Kakakin rundunar yan sanda reshen jahar Kwara, Ajayi Okasanmi, ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai.

Yace mataimakin shugaban ƙungiyar direbobin keke nafef, Ganiyu Adebayo, ya kawo wa yan sanda rahoton yadda lamarin ya faru tsakanin mai motar da kuma ɗan napep.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here