‘Yan IPOB sun Kaiwa Motar Burodi Hari a Enugu

 

Wasu bata gari da ake zargin ‘yan IPOB ne sun kaiwa motar jigilar burodi hari a Enugu.

Bata garin sun fizgo direban motar, suka sace dukkan abinda ke ciki sannan suka kona motar.

Daga bisani sojoji sun iso wurin sun tarwatsa bata garin ta hanyar harba bindiga a sama.

Wasu mutane da ake zargin mambobin haramtaciyar kungiyar masu neman kafa kasar Biafara, IPOB, sun tare wata motar burodi a Enugu sun sace burodin sannan suka bankawa motar wuta a safiyar ranar Talata.

Lamarin ya faru ne a Emene, bayan garin babban birnin Enugu, a ranar da aka umurci mazauna garin su zauna a gida don nuna goyon baya ga Nnamdi Kanu, shugaban IPOB, Daily Trust ta rawaito.

Da ya ke bada labarin, shaidan ya ce:

“Direban shi ke da sanannen gidan burodi na Chimex a unguwar. Sun fito da direban da karfi da yaji, suka sace duka burodin sannan suka kona motar.

“Daga bisani sojoji sun iso wurin sun rika harbi a sama don tarwatsa bata garin. Babu wanda ya mutu. Ina kallon dukkan abin da ke faruwa daga nesa.”

Daily Trust ta tattaro cewa wadanda ake zargin sun kuma sake kona wata motar da babur din adaidaita sahu.

Bata garin sun kai wa direban motan hayar hari sannan suka kona motar bayan korar fasinjojin.

An kona motar, kirar Sienna ne a mahadar Ibeagwa da ke layin Enugu-Opi a karamar hukumar Enugu ta Gabas.

Kazalika, an lalata wasu adaidaita sahu biyu a yankin.

An kona daya ne a mahadar PRODA, Emene yayin da dayan kuma aka kona shi dab da Jami’ar Coal City.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here