Cross Rivers: Kada a Sake a Harbi Masu Diban Kayan Tallafin Korona

Bayan samun labarin ana diban kayan tallafin Korona, gwamnan Cross RIver ya aika sako mai muhimmanci ga jami’an tsaro.

Mai magana da yawun gwamnan ya saki jawabi da yammacin Juma’a – Gwamnan ya ce tuni ya fara raba kayan tallafin a yankunan karkara Gwamnan jihar Cross River, Farfesa Ben Ayade, ya umurci jami’an tsaro kada su harbi kowa a inda matasa ke diban kayan tallafin Korona da gwamnatin ta boye, cewar rahoton Vanguard. A jawabin da mai magana da yawunsa, Mr Christian Ita, ya saki, ya ce gwamna Ben Ayade ya umurci jami’an tsaro da aka tura tabbatar da tsaro a wurare kada su harbi mutanen da suka balla gidan ajiyan abinci. Ya ce gwamnatin ta ajiye kayan tallafin ne domin rabawa mutanen karkara. “Makonni biyu da suka gabata aka kawo mana kayan abincin kuma mun fara rabawa musamman a karkara, ” yace.
“Gwamnan ya ce akwai takaici wasu bata gari sun kwace zanga-zangar lumanan da matasa suka fara kan cin zarafin yan sanda,” Ya yi kira ga kowa a jihar su cigaba da kasancewa cikin zaman lafiya.
Kada a sake a harbi masu diban kayan tallafin Korona – Gwamnan Cross Rivers ya umurci jami’an tsaro credit: @OJay_Jahswill Source: Twitter Mun kawo muku rahoton cewa wasu mutane a jihar Calabar sun afka dakin ajiya kayayyaki da ke Bishop Moynah Street, inda aka ajiye kayan abinci na tallafin annobar korona inda suke ta diban abinda suke so. Mutanen da suka hada da maza da mata suna ta tururuwa zuwa wurin da kayan abincin suke suna diba a kai. Gwamnatin jihar ta tara dubunnan kwalayen Indomie da ya kamata a rabawa mutane lokacin dokar kulle na Korona amma har yanzu ba’a raba ba.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here