Dalilin da Yasa na ki Mallakar Tsayayyen Namiji – ‘Diyar DJ Cuppy

 

Dj Cuppy, diyar shahararren biloniyan nan na Najeriya, Femi Otedola ta magantu a kan dalilinta na rashin mallakar tsayayyen namiji.

Matashiyar ta bayyana cewa duk masu zuwa wurinta ba soyayyarta ke kawo su ba illa kudin mahaifinta.

Ta ce da zaran ta hadu da namiji magana na farko da ke fiotowa daga bakinsa shine yaushe zai hadu da mijinta.

Shahararriyar mai hada sautin kida ta Najeriya, Florence Otedola, wacce aka fi sani da Dj Cuppy, ta magantu game da dalilin da yasa har yanzu bata da tsayayyen namiji.

Cuppy ta bayyana cewa yawancin mazan da ke shigowa rayuwarta ba sonta suke yi da gaskiya ba illa sai don kudin mahaifinta, Nigerian Tribune ta rahoto.

Matashiyar wacce ta kasance diyar shahararren dan kasuwa nan kuma biloniya, Femi Otedola, ba ta ce bata damu da hakan ba illa dai ta mayar da hankalinta wajen ganin mafarkinta ya zama gaskiya da kuma samun ilimi don zama irin macen da take sha’awa.

Budurwar wacce tayi karin haske game da shirinta na komawa makaranta don karantar fannin noma tace ba laifinta bane cewa maza na zuba ido a kan shaharar mahaifinta.

Ta kara da cewa a duk lokacin da ta samu masoyi, tambaya na gaba da yake mata shine “yaushe zan hadu da mahaifinki?”

“Sai na tambayesu menene dalilin da yasa a kodayaushe suke magana game da mahaifina maimakon mayar da hankali a kaina da kuma abun da muke ciki. Ina mamakin dalilin da yasa duk suke mayar da hankali kan haduwa da mahaifina idan muna tattaunawa. Ina mamakin me yasa sunan mahaifina ke shigowa hirarmu

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here