Ambaliyar Ruwa: Sama da Mutane 140 Sun Rasa Rayukansu a Sudan – MDD

Majalisar Ɗinkin Duniya ta tabbatar da cewa sama da mutum 140 ne ambaliyar ruwa ta halaka a Sudan da kuma lalata gidaje 25,000 a ƙasar.

Hukumomi a Sudan ɗin sun bayyana cewa akwai ƙarin gidaje 50,000 da ambaliyar ta yi wa ɓarna duk da ba ta lalata su baki ɗaya ba a jihohi 16 cikin 18 na ƙasar.

Akan soma ruwan sama ne a Sudan a watan Mayu a kuma ƙarƙare a Oktoba.

Ofishin kula da ayyukan jin ƙai na Majaliar Ɗinkin Duniya ya bayyana cewa ambaliyar ruwan ta kawo cikas matuƙa ga karatun yara a ƙasar inda makarantu 125 ambaliyar ta lalata.

Haka kuma ofishin ya bayyana cewa akwai ƙarin barazanar ɓarkewar cutuka musamman a wuraren da ke da akwai cukowar jama’a.Majalisar Ɗinkin Duniya ta tabbatar da cewa sama da mutum 140 ne ambaliyar ruwa ta halaka a Sudan da kuma lalata gidaje 25,000 a ƙasar.

Hukumomi a Sudan ɗin sun bayyana cewa akwai ƙarin gidaje 50,000 da ambaliyar ta yi wa ɓarna duk da ba ta lalata su baki ɗaya ba a jihohi 16 cikin 18 na ƙasar.

Akan soma ruwan sama ne a Sudan a watan Mayu a kuma ƙarƙare a Oktoba.

Ofishin kula da ayyukan jin ƙai na Majaliar Ɗinkin Duniya ya bayyana cewa ambaliyar ruwan ta kawo cikas matuƙa ga karatun yara a ƙasar inda makarantu 125 ambaliyar ta lalata.

Haka kuma ofishin ya bayyana cewa akwai ƙarin barazanar ɓarkewar cutuka musamman a wuraren da ke da akwai cukowar jama’a.

VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here