Legas: Yadda ‘Yan Daba Suka Sace Takardun Makaranta na, Fasfoti da Kayan Abinci#Dan Majalisar
Shugaban masu rinjaye na majalisar jihar Legas, Sanai Ogunbiade, ya ce ‘yan ta’adda sun shiga gidansa na Ikorodu sun yi masa fashi da tsakar rana
Ya wallafa hakan a shafinsa na kafar sada zumuntar zamani ta Twitter, inda yace daukar nauyinsu aka yi don su kasheshi, sai dai basu samu nasara ba – A cewarsa, sun sace masa takardun makarantarsa, fasfotin tafiye-tafiyen iyalinsa, kayan alatun da ke dakin matarsa har da kayan abincin da ke gidansa Shugaban masu rinjaye na majalisar jihar Legas, Sanai (SOB) Agunbiade ya ce an biya batagarin da suka afka wa gidansa da ke Ikorodu a ranar Juma’a ne, don su kashe shi. Agunbiade, dan majalisa mai wakiltar mazabar Ikorodu ta daya, ya ce ya ji kishin-kishin cewa za’a kai masa harin, amma ya zaton duk soki burutsu ne
Read Also:
Ya ce sun iso gidan amma basu sameshi ba, sai suka sace takardun makarantarsa, fasfotin tafiye-tafiyen iyalinsa da sauran abubuwa masu kima a gidansa kamar kayan abinci. Ya wallafa hakan a shafinsa na kafar sada zumuntar zamani ta Twitter, Tha Nation ta wallafa. Makamancin wannan labarin ya yi ta yawo, wanda bata gari suka shiga gidan ajiyar abinci na jihar Legas dake Mazamaza, inda aka ajiye kayan abincin tallafin COVID-19. Ga yadda dai Agunbiade ya wallafa: “Yadda bata gari suka kai wa gidana da ke Ikorodu hari.” Yace: “Godiya ta tabbata ga Ubangiji akan harin da ‘yan ta’addan suka kawo min a ranar Juma’a, 23 ga watan Oktoba bai kai ga rasa rayuka ba. “Na samu labarin za’a kawo min hari, sai dai na dauki maganar a matsayin shirme, don haka ban nemi wasu jami’an tsaro don kula da gidan ba don kada a rasa rayuka. Na yarda da hukuncin Ubangiji a rayuwata. “Dangane da wadanda suka dauki nauyin ‘yan ta’addan saboda sabanin ra’ayi a siyasa, ‘Nagode.’ Mun san junanmu a Ikorodu, amma Ubangiji ne madaukaki, kuma zai yi sakayya ga duk wanda aka zalunta. “Ina farin cikin kasancewa cikin koshin lafiya, har naga ranar 25 ga watan Oktoba da ta kasance zagowar ranar haihuwata. Burin makiya na su kasheni kafin ranar bai cika ba. Nagode wa Ubangiji.”