ɗan Daban Siyasa ya Harbi Mutane 4 a Babban Shagon Kasuwanci da ke Jihar Ondo
Ondo – Wani da ake kyautata zaton ɗan daban siyasa ne ya harbi aƙalla mutum huɗu da bindiga a garin Idanre, hedkwatar karamar hukumar Idanre, jihar Ondo.
Jaridar Leadership ta gano cewa ɗan daban, mamban jam’iyyar APC, ya kutsa kai babban shagon kasuwanci, ‘Supermarket’ a yankin Ojota da nufin yi wa mai wurin fashi.
Mutumin da ake zargin wanda ya fi shahara da sunan, ‘Para’ ya yi ƙaurin suna wajen yi wa mutanen yankin kwace bisa tilas yayin da gwamnati ta kawar da kanta kan abinda yake aikata wa.
Wata majiya ta faɗa wa jaridar cewa:
Read Also:
“A ko da yaushe Para ya saba aikata irin haka kuma gwamnati bata taɓa sa mak ido ba. Yau ya shiga babba shagon Super Market don ya karɓi kudi amma masu wurin suka ƙi ba shi.”
“Mai shagon ya gaya masa cewa yanzun suka fito da safe ba su fara ciniki ba. Yayin suka fara sa’insa da mai wurin, nan take Para ya fizgi jakar mai shagon, suka fara ja-in-ja da shi kan jakar.”
“Kafin mu gano me ke faru, Oara ya zare bindiga ya harbi mutum huɗu nan take. Tuni aka yi saurin kai mutanen Asibitin Idanre, inda yanzu haka suna kwance ana ba su kulawa.”
Shin hukumomin tsaro sun samu rahoto?
Amma da yake tabbatar da aukuwar lamarin, kakakin hukumar yan sandan jihar Ondo, Funmi Odunlami, ya ce Kes din na fashi da makami ne.
Odunlami ya bayyana cewa tuni jami’an yan sanda suka garzaya suka cafke wanda ake zargi da aikata lamarin.
Ku saurari karin bayani…