Murnar Cin Jarrabawa: Matasa 4 Sun Nutse a Ruwa a Jihar Legas

 

Rundunar ‘yan sanda a jihar Legas ta ce wasu matasa hudu sun nutse a ruwa a yayin da suke murnar cin jarrabawar kammala sakandire.

Lamarin ya afku ne a ranar Talata a tekun Elegushi da ke unguwar masu galihu ta Lekki.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan SP Benjamin Hundeyin, ya wallafa a shafinsa na tiwita cewa matasan sun nitse bayan sun karbi sakamakon jarrabawarsu daga makaranta.

Hukumar gudanarwar tekun ta ce mamatan na daga ckin dalibai 10 da suka je wajen don yin murnar samun nasara a jarrabawarsu ta kammala karatun sakandire.

Mai magana da yawun hukumar gudanarwar ya ce yaran sun bijirewa gargadin da jami’an da ke kula da tekun suka yi musu.

Kawo yanzu dai mahukunta ba su bayyana shekarun yaran ba ko kuma daga in da suka fito ba.

Jihar Legas dai na kewaye da ruwa da kuma wuraren shakatawa abin da ya sa mutane kanje don shakatawa ko kuma gudanar da wani biki a bakin teku.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here