2021: Dokoki 8 da Aka Sakawa Masu Aikin Umrah
Musulman da ke shirin yin Umrah a shekarar 2021 za su gamu da dokoki.
Ba za a bar masu yin aikin Umrah su rika taba ka’aba a shekarar nan ba.
Watakila an kawo wadannan dokokin ne domin yaki da cutar COVID-19 Masu zuwa aikin Umrah a wannan shekarar da ake ciki za su gamu da wasu bakin dokoki da maniyyatan kasa mai tsarkin ba su san da su ba.
Rahotanni sun bayyana cewa an kafa wasu sababbin sharuda da dokoki da masu aikin Umrah za su bi wajen ibadar su a wannan shekarar ta bana.
Bayanan da aka fitar a shafin ‘Inside the Haramain’ mai yada labaran abin da su ka shafi aikin Hajji da Umrah ne su ka fito da wadannan dokoki.
Read Also:
Daga cikin sharudan shi ne babu maniyyacin da za a bari ya taba dakin ka’aba a wajen umrah. Haka zalika ba za a bar musulmai su yi zaman masallaci watau ibadar I’tikafi a kwanaki goma na karshen watan Ramadan kamar yadda aka saba ba.
Bisa dukkan alamu an kawo wadannan dokoki ne saboda a takaita yaduwar cutar COVID-19 tsakanin maniyyatan da su ka je yin aikin na umrah.
Ba a za rika taro domin ayi buda-baki, sai dai za a rika raba wa Bayin Allah abincin karya azumi.
Rahoton ya nuna duk musulman da za su yi Umrah a cikin watan na azumi, dole su bi wadannan ka’idoji a zaman su a harami da kuma birnin Makkah.
1. Za a yi sallar Asham a bangaren sharifain
2. An kayyade wuraren da za ayi tarawihi
3. Za a rufe wurin dawafi sai ga masu umrah
4. Masu umrah ba za su taba dakin ka’aba ba
5. Ba za a rika yin jami’i wajen buda baki ba
6. Babu damar I’itiqafi a kwanaki goman karshe
7. Ba za a saki ruwan zam-zama ba, sannan kuma
8. Sai da izini za a iya shiga masallaci mai alfarma