Dole Duniya ta Taimakawa Afghanistan – MDD
Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, ya ce dole ne duniya ta dauki mataki don kaucewa rugujewar Afghanistan ta hanyar shigar da kudi kai tsaye cikin tattalin arzikinta.
Wakilin BBC ya ce tun lokacin da Taliban ta karbi mulki ne aka dakatar da ita daga amfani da kudaden Afghanistan da ke jibge waje, dama hana ta damar samun tallafin daga kasashen duniya.
To sai dai Mista Guterres ya ce za a iya inganta lamarin ba tare da yin katsalandan kan ka’idoji da sanya kudaden a hannun Taliban ba.
Batun yadda za a shawo kan matsalolin kasar ne zai zama babbar ajandar taron kasashen G20 yayin da shugabanninsu za su tattauna ranar Talata.