An ɗage shari’ar  Tsohon Shugaban Burkina Faso, Thomas Sankara 
Kotun soji ta ɗage shari’ar da aka cimma ana dako kan kashe tsohon shugaban da aka hambarar Thomas Sankara.
Bayan daukan lokaci mai tsaho na dambarwa kotun ta ɗage saurar shari’a zuwa mako biyu gaba zuwa 15 ga watan Oktoban 2021.
An kashe Sankara a 1987 a wani kazamin juyin-mulki da mataimakinsa Blaise Comparoe ya jagoranta, wand ake cikin mutum 14 a yanzu da ake tuhuma.
Compaore wanda yanzu haka ke gudun hijira a Cote d’Ivoire bai halarci zaman kotun ba da lauyoyinsa ke cewa akwai siyasa a ciki.
Kotun ta umarci Compaore ya koma kasar nan da kwanaki 10 domin gabatar da kansa a shari’ar.
 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here