‘Yan Bindiga Sun yi Awan Gaba da ɗalibai 3 a Kaduna
Ƴan bindiga sun kai hari wata makarantar Kirista ta ɗariƙar Katolika a jihar Kaduna da ae arewa maso yammacin Najeriya inda suka sace ɗalibai uku tare da ji wa wasu da dama rauni.
Wannan ne hari na baya-bayan nan da ake kai wa kan makarantu inda ake sace ɗalibai don karɓar kuɗin fansa da kashe wasu da ji wa wasu rauni.
Wani mai magana da yawun rundunar ƴan sanda jahar Kaduna ya shaida wa BBC cewa mahara a kan babura ne suka dirar wa makarantar ta Saint Albert Seminary a garin Kagoma a ranar Litinin da daddare inda suka buɗe wuta tare da sace ɗalibai sannan suka gudu.
Tuni aka kai wadanda suka ji rauni zuwa asibiti yayin da aka fara neman waɗanda aka sace ɗin a dajin da ke kusa da yankin.
Satar mutane don kuɗin fansa ya zama ruwan dare a Najeriya, kuma na sace kusan ɗalibai 1500 daga makarantu da jami’o’i daban-daban tun watan Disamban bara.
An saki mafi yawansu bayan sasantawa da ƴan bindigar amma har yanzu akwai gwammai dƴan makarantar Yuri da ke hannun ƴan bindigar.
 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here