Tsohon Mataimakin Babban Bankin Najeriya Dr Obadiah Mailafia, Ya Rasu
Tsohon mataimakin Babban Bankin Najeriya Dr Obadiah Mailafia, ya rasu kamar yadda matarsa ta tabbatar wa BBC.
Ta ce ” ya rasu ne a asibitin Gwagwalada da safiyar Lahadi bayan gajeruwar rashin lafiya.”
Sai dai ba ta bayyana rashin lafiyar da ta yi ajalinsa ba, tana mai cewa binciken asibiti bai kai ga tabbatar da abin da ya yi ajalinsa ba.
Read Also:
Obadiah Mailafia ɗan asalin jahar Kaduna ne kuma masanin tattalin arziki ne da harakokin banki.
Ya rike mukamin mataimakin Babban Bankin Najeriya tsakanin shekarar 2005 zuwa 2007.
Marigayin ya taɓa tayar da ƙura a Najeriya, a wata hira da aka yi da shi inda ya yi zarge-zarge da dama, ciki har da zargin ɗaya daga cikin gwamonin arewacin Najeriya da jagorantar ƙungiyar Boko Haram.
Sai dai daga baya Obadiah ya ce a kasuwa ya tsinci zancen a bakin wasu Fulani.