Abubuwa Game da Marigayi Dr Obadiah Mailafia

 

A yau ne aka samu mummunan labarin mutuwar wani jigo a Najeriya, tsohon mataimakin gwamnan babban bankin Najeriya, Dr Obadiah Mailfaia. Ya taka rawa a Najeriya ta fuskoki da dama.

A cikin wannan rahoton nan, Legit.ng ta kawo muku wasu abubuwa da kuke bukatar sani game da Dr Obadiah Mailafia.

Bayanai kan Dr Obadiah Mailafia

1. Ya kasance tsohon mataimakin gwamnan babban bankin Najeriya (CBN).

2. Ya kasance dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar ADC a zaben 2019.

3. An haifi Mailafia a ranar 24 ga Disamba, 1956, a Karamar hukumar Sanga ta jahar Kaduna.

4. Ya kammala digirinsa na farko a Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya, a shekarar 1978 inda ya karanta kimiyyar zamantakewa (Siyasa, Tattalin Arziki, da Ilimin zamantakewa).

5. Ya kuma yi digiri na biyu a fannin na tattalin arziki.

6. Ya tafi zuwa kasar Ingila, Kwalejin Oriel, inda ya sami digirin digirgir daga Jami’ar Oxford a 1995.

7. Ya shiga harkar siyasa a shekarar 2018 sakamakon karuwar kashe-kashe a Kudancin Kaduna.

8. Ya taba zargin wani gwamnan arewa cewa shine kwamandan Boko Haram.

9. Biyo bayan furucinsa kan Boko Haram, hukumar DSS ta gayyace shi ofishinta

10. Daga baya ya lashe amansa

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here