DSS ta Sako Shugaban Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa, Ajaero

 

Hukumar Tsaro ta DSS ta sako Shugaban Ƙungiyar Ƙwadago ta Ƙasa (NLC), Joe Ajaero, kimanin mintoci 35 kafin cikar wa’adin da ƙungiyar ta bayar.

A cikin dare ne dai hukumar ta sako Ajaero, a kan beli, gabannin cikar wa’adin ƙarfe 12 da ƙungiyar na sakin sa.

NLC da ƙungiyoyin ma’aikata sama a 50 da ke ƙarƙashinta sun yi barazanar yajin aiki da zanga-zangana faɗin Najeriya idan har 12 na dare yi ba a sako shi ba.

Kafin cikar wa’adin ne Ajaero ya sanar ta shafi da na X cewa, “Gwmanatin Tinubu ta sako shugaban NLC Ajaero daga ofishin DSS a kan beli,” in ji shi.

Jami’an hukumar DSS sun kama Ajaero ne da sanyin safiyar Litinin din a filin jirgin sama da ke Abuja, a hanyarsa ta zuwa taron Ƙungiyar Ƙwadago ta Duniya a ƙasar Birtaniya.

Kwanaki 10 ke nan bayan ’yan sanda sun yi masa tambayoyi kan zargin ɗaukar nauyin ta’addanci, a ranar 29 ga watan Agusta.

NLC da kungiyoyin kare hakkin ɗan Adam da dama, sun yi tir da lamarin tare da kira ga hukumar ta gaggauta sako shi.

Jim kadan da haka ne dai jami’an DSS suka kai wani samame ofishin kungiyar SERAP mai bibiyar kashe kuɗaɗen gwamnati da ke Abuja, suna neaman shugaban cibiyar.

Wannan dai ya jawo wa hukumar cacckar daga ƙungiyar mnesty International, wadda ta ce matakin ya nuna Gwamnatin Tunubu taba wuce gona da iri.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here