Ministan Ayyuka na Musamman ya Bukaci Hukumar EFCC da ta Binciki Gwamna Ortom
Ministan ayyuka na musamman, kuma tsohon gwamnan Benuwai, Akume, ya yi kira ga EFCC ta binciki Ortom.
Ministan ya kuma bukaci gwamna Ortom na jahar Benuwai ya fito ya baiwa shugaba Buhari hakuri.
Sanata George Akume ya yi wannan kiran ne a wani taron manema labarai da ya samu halartar kusoshin APC a Benuwai.
Abuja – Ministan ayyuka na musamman da harkokin gwamnati, Sanata George Akume, ya bukaci hukumar yaki da cin hanci EFCC ta fara bincikar gwamnan Benuwai, Samuel Ortom.
Sanata Akume, wanda tsohon gwamnan Benuwai ne, ya yi wannan kiran ne a wani taron manema labarai a Abuja, kamar yadda dailytrust ta rawaito.
Ministan yace:
“Muna kira ga hukumomin yaki da cin hanci da rashawa EFCC da ICPC su tsananta bincike kan yadda akai da kasafin kuɗin tarayya na jahar Benuwai tun daga 29 ga watan Mayu 2015 zuwa yanzu.”
Read Also:
“Ya kamata gwamnatin tarayya cikin gaggawa ta bada umarnin dakatar da kason tsare dabbobi na jahar Benuwai bisa hannun gwamnatin jahar wajen aikata manyan laifuka.”
“Wanda hakan ke haddasa rashin zaman lafiya da kwanciyar hankali ga mazauna jahar da ba su ji ba kuma basu gani ba.”
Gwamna Ortom ya baiwa Buhari hakuri
Hakanan kuma ministan ya nemi gwamna Samuel Ortom ya fito ya baiwa shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, hakuri kuma ya dakatar da sukar da yake masa.
Gwamna Ortom ya jima yana takun saka da fadar shugaban ƙasa kan rikici tsakanin fulani da makiyaya da kuma matsalar tsaron da ta addabi jahar.
Hakanan kuma ministan ya nemi gwamna Samuel Ortom ya fito ya baiwa shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, hakuri kuma ya dakatar da sukar da yake masa.
Gwamna Ortom ya jima yana takun saka da fadar shugaban ƙasa kan rikici tsakanin fulani da makiyaya da kuma matsalar tsaron da ta addabi jahar.
Akume yace:
“Muna kira ga gwamna Samuel Ortom ya baiwa shugaba Buhari hakuri saboda amfani da kalaman da ba su dace ba, da kuma shiga harkokin da basu shafe shi ba tsakanin jiha da gwamnatin tarayya.”
Legit.ng Hausa ta gano cewa taron manema labaran ya samu halartar kusoshi da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC reshen jahar Benuwai.