Zambar Intanet : EFCC ta ƙama Mutane 21 a Abuja
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya EFCC, ta ce ta kama mutum 21 da ake zargi da aikata zamba ta intanet a Abuja.
Read Also:
A wani sako da EFCCn ta wallafa a shafinta na twita, ta ce ta kama mutanen ne a unguwannin Kubwa da Lugbe bayan samun bayanan sirri kan ayyukan da suke aikatawa.
Ta ce ta gano manyan wayoyin salula na zamanai guda 25 da motoci ƙirar Mercendes da kuma kwamfutocin tafi-da-gidanka guda uku a hannun waɗanda take zargin.
EFCC ɗin ta kara da cewa za a tura mutanen zuwa kotu da zarar an kammala bincike.