Yawan Fararen Hula da Suka Rasa Rayukansu a Rikicin Sudan

 

Kungiyar likitoci a Sudan ta ce alkaluman fararen hula da suka mutu a rikicin ƙasar da ake ci gaba da yi, ya kai 822, tare da jikkata wasu mutum 3,215.

Faɗan da ya barke a ƙasar a ranar 15 ga watan Afrilu na ci gaba da munana duk da tattaunawar sulhu da ake yi a birnin Jeddah na Saudiyya da kuma yarjejeniya da aka cimma na bai wa fararen hula kariya da kai kayan agaji a ranar 11 ga watan Mayu.

“Birnin El-Geneina da ke yammacin Darfur ya fuskanci tashin hankali mafi muni tun lokacin da aka fara rikicin…inda aka kashe mutum 280 da jikkata 160 a cikin kwanaki biyu kaɗai,” in ji kungiyar likitoci a ranar Talata.

A cewar kungiyar, wasu biranen da fararen hula suka mutu sakamakon rikicin ya haɗa da Khartoum, babban birnin ƙasar da biranen Bahri da Omdurman da El Obeid da kuma Arewacin Kordofan.

Rikicin wanda ke shiga wata na biyu, ya ɗaiɗaita mutane kusan rabin miliyan daga gidajensu, a cewar Majalisar Ɗinkin Duniya.

 

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here