Ƴan Bindiga Sun Kai Hari Kan Ayarin Motocin Ofishin Jakadancin Amurka a Najeriya, An Kashe Mutane 4

 

Ƴan sanda a Najeriya sun ce ƴan bindiga sun kai hari kan ayarin motocin ofishin jakadancin Amurka a ƙasar, inda aka kashe mutum huɗu, ciki har da jami’an karamin ofishin jakadancin Amurka biyu da kuma ƴan sanda guda biyu.

An kuma yi garkuwa da wasu mutum uku kafin daga bisani a cinna wa motarsu wuta.

Harin ya auku ne a ranar Talata a jihar Anambra da ke kudu maso gabashin Najeriya. A yanzu dai an kaddamar da shirin ceto.

Sai dai babu Ba’amurke ko ɗaya da harin ya rutsa da shi.

Rundunar ƴan sandan Najeriya reshen jihar ta nuna ɓacin rai na cewa ba a tuntuɓe ta ba a lokacin da kwambar motocin ta isa jihar domin samun kariya.

Amurka ta ce tana aiki da jami’an tsaron Najeriya domin yin bincike kan lamarin.

health blogs guest post

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here