Fintiri ya Karɓi Shaidar Cin Zaɓe

 

Zaɓaɓɓen gwamnan jihar Adamawa Ahmadu Umaru Fintiri da mataimakiyarsa Farfesa Kaletapwa Farauta sun karɓi takardun shaidar cin zaɓensu a shalkwatar hukumar zaɓen ƙasar da ke Abuja.

Hukumar zaɓen ƙasar ta ba su takardun shaidar cin zaɓen ne da maraicen ranar Laraba a Abuja.

A ranar Talata ne hukumar zaɓen ƙasar ta sanar da gwamna Ahmadu Umaru Fintiri a matsayin wanda ya lashe zaɓen jihar, da ya ƙare cikin taƙaddama.

Jami’in sanar da sakamakon zaɓen gwamna na Adamawa, Farfesa Mohammed Mele ya ce Ahmadu Fintiri ya yi nasarar lashe zaɓen ne da ƙuri’a, 430, 861.

Gwamnan mai ci ya samu nasara a kan babbar abokiyar fafatawarsa Aisha Ɗahiru Binani wadda ta samu ƙuri’a, 398, 788.

Wannan nasara ta bai wa Fintiri ikon ci gaba da mulkin jihar Adamawa a wa’adi na biyu.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here