Ganduje ya Gabatar da Wata Muhimmiyar Bukata a Gaban Rarara da Ali Nuhu
Read Also:
Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano, ya tunkari masana’antar shirya fina-finai domin su taimaka masa wajen tabbatar da zaman lafiya a jiharsa.
Ganduje ya nemi Rarara da Ali Nuhu su yi amfani da kwarewarsu wajen shirya fim da yin wakar wayar da kai ga al’umma don jadadda masu muhimmancin zaman lafiya – Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ake samun tashe-tashen hankula a wasu sassan kasar sakamakon zanga-zangar EndSARS Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje, a kokarin da yake na ganin an samu zaman lafiya a jihar, ya roki kungiyar masu shirya fina-finan Hausa da na mawaka a kan su yi amfani da kwarewarsu wajen wayar da kan al’umma game da muhimmancin zaman lafiya. Ya yi wannan kira ne a yayin waata ganawa da ya yi da kungiyar MOPAN a ranar Talata, a daki taro na Africa House da ke gidan gwamnatin jihar, jaridar Aminiya ta ruwaito.
A cikin jawabin nasa, gwamnan ya yi kira ga shahararren mawakin nan na siyasa, Dauda Kahutu wanda aka fi sanda da Rarara, a kan ya rera wakokin wayar da kai ga jama’a kan muhimmancin zaman lafiya
Har ila yau, ya bukaci fitaccen jarumi a masana’antar Kannywood, Ali Nuhu, da ya shirya fina-finan wayar da kan al’umma kan fa’idar zaman lafiya. Ana dai ta fuskantar rashin zaman lafiya a wasu jihohin kasar sakamakon zanga-zangar EndSARS da aka fara gudanar da ita makonni biyu da suka gabata.