Gwamna Ganduje ya Karbi Fom Din Takarar Sanata

Ganduje ya shiga jerin gwamnonin dake neman komawa majalisa bayan karewar wa’adinsu a 2023.

Ganduje zai yi takara da Sanata Barau Jibrin a zaben tsayar da gwanin da za’a yi makonni masu zuwa.

Gwamnan na Kano ya zabi mataimakinsa Gawuna ya gajesa, kuma kwamishanan Garo matsayin mataimakinsa.

Kano- Gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya karbi Fom din takara kujerar Sanata na jam’iyyar All Progressives Congress (APC).

Dan siyasan mai shekaru 72 a duniya na shirin wakiltar mazabar Kano ta Arewa majalisar dattawan tarayya.

Ganduje, zai kara da Sanata Barau Jibrin wanda ke rike da kujeran tsawon shekaru bakwai yanzu.

Ganduje ya rike matsayin mataimakin gwamna karkashin Rabiu Kwankwaso 1999-2003 sannan suka sake tafiya tare 2011-2015.

Ya gaji maigidansa na lokacin inda ya lashe zaben gwamnan jihar a 2015 kuma ya sake cin zabe a 2019.

Idan ya kammala wa’adinsa a 2023, yana niyyar cigaba da kasancewa a gwamnati.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here