Yadda Aka Gano Lauyan Bogi da ya yi Nasarar Lashe Kararraki 26 a Kotu
Wani mutum da ake zargin lauyan bogi ne ya kare wasu mutane a gaban kotu kuma ya yi nasarar lashe kararraki da dama.
Mutumin mai suna Brian Mwenda Njagi ya tsayawa mutane a kararraki 26, kuma gaba daya shine a sama.
Asirin Brian ya tonu ne bayan kungiyar lauyoyi a yankin ta gano cewa yana yiwa wani lauya sojan gona ne.
Wani mutumi wanda ake zargin lauyan bogi ne ya yi nasarar lashe kararraki 26 a kotu kafin aka gano shi.
An yi zargin cewa mutumin, Brian Mwenda Njagi, yana yi wa wani lauya mai irin sunansa sojan gona ne.
Kamar yadda kungiyar lauyoyin na Kenya ta bayyana, ainahin lauyan da ake yi wa sojan gona sunansa Brian Mwenda Ntwiga.
Lauyan bogi ya wakilci mutane a kotu kuma ya yi nasara a kararraki
Ainahin lauyan, Brian Mwenda Ntwiga, ya samu shiga kungiyar amma ba a riga an ba shi satifiket dinsa na fara aiki ba.
An rahoto cewa shi lauyan na bogi, Brian Mwenda Njagi, ya samu yin kutse a shafin yanar gizon kungiyar sannan ya nemi satifiket din fara aiki da bayanan ainahin lauyan.
Read Also:
“A ranar 5 ga watan Agustan 2022, Brian Mwenda Ntwiga ya samu shiga kungiyar lauyoyi kuma an dauki bayanan ainahin shafinsa na imel sannan aka bude masa shafi a shafin yanar gizon kungiyar.
“Mun tuntubi Brian Mwenda Ntwiga, wanda ya tabbatar da cewar bai nemi a yi masa satifiket din fara aiki ba tun bayan shigarsa kungiyar, dalili kuwa shine cewa yana aiki a ofishin Atoni Janar kuma baya bukatar satifiket din fara aiki.
“Har sai da wani lokaci a Satumban 2023 lokacin da ya yi yunkurin shiga shafin da kuma farfado da bayanansa da nufin neman satifiket din fara aiki, a lokacin ne ya gane cewa ya gasa shiga shafin nasa.”
Brian Mwenda Njagi ya yi wa wani lauya sojan gona
Da fara bincike sai aka gano cewa shi lauyan bogin, Brian Mwenda Njagi ya sauya hoton ainahin lauyan sannan ya sanya nasa a shafin yanar gizon kungiyar.
Kungiyar lauyoyin ta yi kira ga kama Brian Mwenda Njagi. Labarin ya yadu, kuma Naira PR ta wallafa shi a dandalin X, kuma ya samu martani da dama.
Jama’a sun yi martani
@Iselema ya ce:
“Ku tura shi makarantar lauyoyi, kwararren lauya ne mara digiri.”
@godsentkalu123 ta ce:
“Kawai a mallaka masa shaidar digiri a bangaren karatun lauya.”
@Oluchima1 ta ce:
“Irin wadannan mutane ba a hukunta su. Maimakon haka a taimaka masa ya zama tauraron da yake son zama.”