Rundunar Sojin Isra’ila na Shirin Kai Hare-Hare a Gaza ta Sama, Kasa da Ruwa

 

Rundunar sojan Isra’ila ta ce tana shirin faɗaɗa yaƙin da take yi a kan Zirin Gaza ta ruwa, da sama, da ƙasa.

“IDF [sojin Isra’ila] na shirin ƙaddamar da babban samame” tare da taimakon sojojin ko-ta-kwana, a cewar wata sanarwa daga rundunar.

Ba a faɗi lokacin kai hare-haren ba amma da ma can ana tsammanin Isra’ila za ta kai hari ta ƙasa cikin Gaza, inda ta umarci mazauna birnin su fice daga arewaci zuwa kudanci.

Ta ce tana shirya wani samame “ta sama, da ruwa, da ƙasa, in ji sanarwar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com