Gawuna ya yi Rantsuwa Kan Rikewa Gwamna Ganduje Amanarsa
Mataimakin gwamnan jihar Kano, Nasiru Yusuf Gawuna, ya yi rantsuwa da Allah cewa zai rikewa Gwamna Abdullahi Ganduje amanarsa.
Gawuna ya dauki alwashin ne a yayin da gwamnan ya gabatar masu da fom din takarar gwamna shi da Murtala Garo.
Ya kuma roki ‘ya’yan jam’iyyar APC da kada su kawo masu munafirci da cin amana a harkokinsu.
Kano- Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya gabatar da fom din takarar gwamna ga mataimakinsa, Nasiru Yusuf Gawuna da tsohon kwamishinansa, Murtala Sule Garo a matsayin abokin takararsa.
Ya gabatar masu da fom din takarar ne a taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a garin Kano a ranar Talata, 10 ga watan Mayu.
Read Also:
Da yake jawabi jim kadan bayan mika musu fom din takarar, Gawuna ya yi godiya ga Ganduje tare da daukar rantsuwar rike ma ubangidan nasa amana, sashin Hausa na BBC ya rawaito.
Gawuna ya ce:
Billahil lazi la ilaha illahuwa mai girma gwamna za mu rike maka amanarka, za mu yi tafiya irin wadda kake so.
“Kuma bi izinillahi kai ma Allah zai cika maka bukatarka.”
Gawuna ya kuma roki ‘ya’yan jam’iyyarsu ta All Progressives Congress (APC), da kada su yi munafinci ko cin amana a lamuransu.
BBC Hausa ta kuma nakalto yana cewa:
“Ina rokon ‘yan jam’iyyarmu da muka hadu a nan, na hada ku da girman Allah yadda mai girma gwamna ya hada ni da dan uwana, shi ya san amanar da ke tsakanina da shi, don Allah don Annabi ka da wanda ya kawo mana annamimanci.”