Yar Sarkin Japan, Gimbiya Mako ta Auri Talakanta

 

Gimbiya Mako ta Japan ta auri abin ƙaunarta kuma talakanta Kei Komuro – lamarin da ya sa ta rasa martabarta da sarautarta.

A dokar Japan, mace ƴar gidan sarauta dole ta bar muƙaminta idan dai har ta zaɓi auren talakanta, sai dai ba haka lamarin yake ga maza ba.

Ta kuma ƙi yin abubuwan da al’ada ta tanadar na auren sannan ta ƙi karɓar kuɗaɗen da ake bai wa ƴan gidan sarautar mata idan za su bar zuri’ar.

Ita ce mace ta farko daga masarautar da ta ƙi karɓar waɗannan abubuwa biyun.

Ana sa ran za su koma Amurka bayan auren – inda Komuro ke aiki a matsayin lauya. Auren nasu ya sa mutane suna ta haɗa shi da na gidan sarautar Birtaniya na Meghan Markle da Yarima Harry, inda har ake wa ma’auratan laƙabi da Harry da Meghan ɗin Japan.

A shekarar 2017, lokacin da Mako, gimbiyar Japan a wancan lokacin, ta sanar da baikonta da wani tsohon ɗan ajinsu a makaranta, Kei Komuro, ta ce ta samu cikar burinta “da salon murmushinsa mai kamar hasken rana.”

Masoyan biyu sun hadu ne shekara biyar kafin 2017 a lokacin da suke ɗalibai a jami’a, inda suka bayyana tsare-tsaren aurensu a shekara ta gaba.

Hakan na nufin gimbiyar za ta zama talakar ƙasa kamar kowa saboda masarautar ƙasar kan ƙwace matsayin duk wata mace ƴar zuri’ar da ta auri talakanta.

Murmushinsu ya saye zuciyar ƴan ƙasar da ake bin diddigin ƴan gidan sarauta kuma ake sa ran iyalan gidan za su zama masu kare al’adu. Yawanci rahotannin da kafafen yaɗa labarai suka yi ta watsawa mai kyau ne.

Amma hakan ya sauya nan da nan.

Wata biyu bayan nan, rahotannin farko suka bayyana kan wani zargin rikicin kuɗi tsakanin mahaifiyar Mr Komuro da tsohuwar budurwarsa, wacce ta yi ikirarin cewa uwa da ɗanta sun gaza biyanta wani bashi da take bin su.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here