Zambar Intanet: An kama mutane 150 

 

Rundunar ‘yan sandan Tarayya Turai wato Europol, ta sanar da cafke mutun 150 da ake zargi da saye da sayar da haramtattun kayayyaki ta wani shafin intanet da ake kira dark web.

Wannan ya biyo bayan rufe wani babban shafin kasuwanci na intanet da ake kira – bakar kasuwa, wato Dark Market tun daga watan Janairu.

Waɗanda aka cafke mutane ne da ake zargi ko kyautata zaton suna cinikin ta wannan shafin.

Wannan shi ne samame mafi girma da aka kai kan masu aikata irin wannan laifi a shafin intanet.

An cafke mutanen ne a kasashen Amurka da Australia da Burtaniya da Jamus da wasu kasashen Turai.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here