An Bayar da Belin Shahararren Mawakin Ghana, Shatta wale 

Wata kotu a birnin Accra ta bayar da belin shahararren mawakin nan na Ghana Shatta Wale a kan kudi sidi dubu 100, kwatankwacin sama da dala dubu 16, yayin da aka bayar da belin yaransa biyu kowannen su a kan dala dubu 100.

A yau ne mawakin mai janyo ce-ce-ku-ce ya bayyana a gaban kotun karo na biyu bayan an ki bayar da belinsa, bayan ya shafe kwana biyar a gidan kaso, biyo bayan tuhumar da ake yi masa na watsa labarin ƙarya cewa an harbe shi.

Ana tuhumar mawakin ne mai janyo ce-ce-ku-ce da laifin ƙoƙarin tayar da zaune tsaye da jefa fargaba a zukatan jama’a bayan ya yada labarin ƙanzon kuregen cewa wasu mutane biyu sun harbe shi a unguwar East Legon da ke birnin Accra.

Sai dai mawakin ya ƙi amsa laifinsa a gaban kotun wadda ta bayar da belinsa inda zai sake bayyana a gaban ta ran 9 ga watan nuwambar 2021 don cigaba da shari’a.

A makonnin da suka gabata ne Shata Wale ya wallafa a shafin zumunta na Facebook cewa wasu mutane sun harbe shi, lamarin da mawakin ya ce ya yi ne saboda hukumomi sun kasa ba shi cikakken tsaro bayan hasashen wahayin da wani malamin kirista ya yi na cewa an harbe mawakin.

Sai dai idon mawakin ya raina fata ne bayan rundunar ƴan sandan Ghana ta fara nemansa ruwa a jallo bayan ta cafke malamin kiristan da yayi hasashen mutuwarsa, abin da ya sa daga baya ya miƙa kansa, in ji mawakin.

Yayin da wasu mutane ke ganin wannan zai zama jan kunne ga mawakin wasu na sarawa sabon shugaban ƴan sanda ne saboda salon sa na ba sani ba sabo.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here