Gwamnatin Gombe ta Saka Hannun a Kasafin Kudin 2021, Za ta Dawo da Biyan mafi ƙarancin albashi

Gwamnatin jahar Gombe ta sanar da cewa zata ci gaba da biyan mafi ƙarancin albashi.

Gwamnan jahar ya sanya hannu a kasafin kudin 2021 ciki har da mafi ƙarancin albashin.

Gwamnatin ta kuma rage kudin gudanar mulki daga 25% zuwa 10% .

Jaridar Daily Trust ya ruwaito cewa, Gwamnatin jahar Gombe ta ce za ta ci gaba da biyan sabon mafi karancin albashi ga ma’aikatan gwamnati a jahar daga watan Janairun 2021.

Kwamishinan kudi da ci gaban tattalin arziki na jahar, Muhammad Gambo Magaji, ya bayyana hakan yayin bayar da ragin kasafin kudin jihar na 2021 da Gwamna Inuwa Yahaya ya sanya hannu.

Gwamnatin jihar a watan Maris na shekarar 2020 ta dakatar da biyan N30,000 a matsayin mafi karancin albashi bayan ta biya na tsawon wata guda, tana mai bayyana dalilan raguwar kudaden shiga.

Magaji ya bayyana cewa kasafin kudin na 2021 ya kama sabon mafi karancin albashi, yana mai cewa shi ne dalilin da ya sa yawan ma’aikata a kasafin da aka amince ya tashi.

Ya kuma bayyana cewa don inganta jin dadin mazauna, an rage kudin gudanar da mulki zuwa kasa da kashi 10 cikin 100 na dukkan kasafin kudin, “sabanin tsohuwar gwamnatin da ta kashe kashi 25 cikin 100.”

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here