Kamfanin Google Zai Zuba Hannayen Jari a Afrika
Kamfanin Google ya sanar da zuba hanayen jarin dala biliyan guda a Afirka a wani ɓangaren na bunkasa ayyukansa a nahiyar.
Read Also:
Shugaban kamfanin Sundar Pichai ya ce za a kashe waɗannan kudade ne a cikin shekaru biyar domin ayyuka daban-daban wanda zai taimaka wa ci gaba fasaha da shafin tsakanin ‘yan Afirka.
Wannan shi ne shiri mafi girma da kamfanin na Amurka ke kaddamarwa a Afirka, da zai taimakawa nahiyar kara samun damar amfani da shafukan intanet cikin sauki da rahusa.
Kasashen da za su ci moriya sun hada da Ghana da Kenya da Najeriya da kuma Afirka ta Kudu.